in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar wakilan kasar Sin ta dudduba gyararren shirin dokar kare ikon masaya, kare muhalli da dai sauransu
2013-10-21 16:17:44 cri

An shirya cikakken taro karo na farko na babban taro na 5 na kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 12 a ran 21 ga wata da safe a birnin Beijing, inda aka dudduba gyararren shirin dokar kare ikon masaya, kare muhalli da dai sauransu.

A cikin gyararren shirin dokar kare ikon masaya da aka dudduba har sau uku, an tabbatar da nauyin da ke bisa wuyan 'yan kasuwa da ke sayar da kaya, haka kuma an kyautata tsarin dawo da kaya ba tare da wasu dalilai ba game da kayayyakin da aka saya ta shafin internet, kuma an sanya sharadi ga kamfanonin da ke sayar da kaya a kan internet da su biya diyya ga masaya kafin a tabbatar da nauyinsu, har ila yau an kyautata wasu ka'idoji kan diyyar da 'yan kasuwa za su biya masaya bayan hukuncin da aka yanke musu.

An kara wasu ka'idoji a cikin gyararren shirin dokar kare muhalli da aka dudduba har sau uku, wato gwamnati za ta kara zuba jari domin kare muhalli, kuma an amince da hukumomin kare muhalli da su samu ikon aiwatar da doka, kuma za a kafa wani tsarin ba da kudin tallafi domin daidaita yanayin zamantakewar dan Adam cikin dogo lokaci, da kuma kara kare muhallin kasa, da kara tafiyar da tsarin tuhumar laifuffuka dangane da harkokin kare muhalli.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China