in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata an gudanar da harkokin kasar Sin bisa mulkin kasa, in ji Zhang Dejiang
2013-03-19 16:23:15 cri
Yau Talata 19 ga wata a nan birnin Beijing, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang ya nuna cewa, gudanar da harkokin kasar Sin bisa doka da shari'a hanya ce da ta dace wajen tabbatar da bunkasuwar kasa mai wadata,  al'umma mai jituwa da kuma kawo amfani ga jama'ar. Ya ce, abin da aka sa gaba shi ne gudanar da harkokin kasa bisa tsarin mulkin kasar.

A safiyar wannan rana ne aka kira taron farko na sabon zaunannen kwamitin majalisar wakilian jama'ar kasar Sin a birnin Beijing, wanda Zhang Dejiang ya jagoranta tare da jin jawabi. Inda a cikinsa ya jaddada cewa, kwamitin ya dauki nauyin dake bisa kansa na bullo da shari'a da doka da kuma tabbatar da aiwatar da su yadda ya kamata. A cikin shekaru biyar masu zuwa, za a mai da hankali wajen tafiyar da harkokin kasa bisa doka da shari'a tare da kiyaye tsarin mulkin kasar a matsayin muhimmin aikin majalisar da kwamitin ta yadda za a ba da taimako ga raya al'ummar kasar Sin irin na gurguzu bisa shari'a da doka. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China