in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu wani wuri a duniya da masu cin hanci za su fake, in ji kakakin kasar Sin
2015-03-31 20:07:48 cri

Yayin da kasar Sin ke aiwatar da aikin da aka yi wa lakabi da "Sky Net" na kama masu cin hanci da karbar rashawa a duk fadin duniya, an labarta cewa, kasar ta Sin ta gabatarwa kasashen Amurka, da Birtaniya, da sauran kasashe takardun sunayen jami'anta, wadanda ake tuhuma da laifin cin hanci, wadanda kuma gwamnatin Sin ke burin dawo da su daga kasashen ketare domin su fuskanci hukunci.

Dangane da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana cewa aikin na "Sky Net", muhimmin mataki ne da kasar Sin ta dauka kan masu cin hanci da karbar rashawa, wadanda suke samun mafaka a kasashen ketare.

Hua wadda ta bayyana hakan a Talatar nan a nan Beijing, ta kara da cewa kasashen duniya sun cimma daidaito kan inganta hadin gwiwa da juna, wajen kame wadanda suka aikata laifukan cin hanci da karbar rashawa, domin dawo da kudaden da suka yi awon gaba da su.

Ta ce duk duniya babu wata kasa wadda take fatan zama Aljannar duniya ga masu cin hanci da karbar rashawa. Don haka gamayyar kasa da kasa ke fatan inganta hadin gwiwa a fannin yaki da cin hanci.

A hannu guda kasar Sin na da burin kara hada kai da kasashen da abin ya shafa a wannan fanni. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China