in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen Afrika da su magance cin hanci a bangarorin gine-gine da sufuri
2013-09-25 10:40:43 cri

Wani babban jami'in gwamnati a kasar Tanzaniya a ranar Talatan nan ya bukaci kasashen Afrika da su hada gwiwwa wajen magance matsalar cin hanci da ya addabi bangaren gine-gine da na sufuri domin wannan dabi'a tana kawowa tabarbarewar tattalin arziki a nahiyar.

Mataimakin ministan ayyuka na Tanzaniya Gerson Lwenge ya bukaci hakan a Arusha lokacin da yake jawabi a wani taron kasa da kasa game da lura da ayyukan gina hanyoyi da lura da sufuri.

Wannan taron da ya shafi kasashe 25 na duniya, kungiyar lura da hanyoyi ta duniya ne ta shirya shi tare da hadin gwiwwar kungiyar hukumomin lura da hanyoyi ta kasashen kudancin Afrika.

Mr. Lwenge ya ce, kasashen Afrika, musammam na yankin dake kudancin Saraha suna gwagwarmayan ganin sun samar da hanyoyi masu inganci da kuma ababen sufuri, sai dai babbar matsalar ita ce cin hanci ya yi katutu a bangaren wanda yake kawo babban illa da durkushewar duk wani shiri mai kyau a kasashen.

Ya ce, lokaci ya yi da kasashen za su hada gwiwwa su yi aiki tare domin dakile wannan babban kalubale wanda ke kawo durkushewar tattalin arzikin kasashen, ganin ayyukan gine-gine yana bukatar kudi mai yawa. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China