Kasar Uganda ta kaddamar a ranar Talata da wani shiri na shekaru biyar domin yaki da matsalar cin hanci dake kamari a cikin kasar, lokacin da ake tunawa da ranar kasa da kasa ta yaki da cin hanci.
A cewar Selon Simon Lokodo, ministan kasa kan bin doka, gwamnatin kasar ta bullo da wani shiri na shekaru biyar mai taken "dabarar kasa ta yaki da cin hanci domin karfafa yaki da cin hanci". Wannan dabara na samar da wani tsarin kasa domin aza hanyar siyasun gwamnati, tsare-tsare da ayyukan ma'aikatun gwamnati daban daban, jihohi, da ma gwamnatocin yankunan kasar baki daya wajen yaki da matsalar cin hanci.(Maman Ada)