in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Afirka ta Kudu za ta bullo da sabon tsarin bayar da kwangila a kasar
2014-02-17 10:41:42 cri

Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, ya bayyana kudurin gwamnatinsa na bullo da sabon tsarin bayar da kwangila a matsayin wani mataki na kakkabe cin hanci da rashawa da ya addabi bangaren aikin gwamnatin kasar.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin wata hira da kafar yada labarun kasar (SABC), inda ya ce, sabon tsarin, zai ta'allak ne ga hukuma guda da za ta rika kula da harkokin kwangilar kasar, matakin da shugaban ya ce, zai taimaka wajen bankado cin hanci cikin sauki.

Shugaba Zuma ya ce, matsalar ta kunno kai ne, sakamakon matakai da dama da ake bi kafin a bayar da kwangila a kasar, abin da ya sa jami'an gwamnati da ke kula da wadannan kafofi ke karbar na goro kafin a bayar da kwangila.

Binciken da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa da kasa ta yi a shekarar 2013, ya nuna cewa, kusan kashi 50 cikin 100 na 'yan kasar Afirka ta Kudu sun bayar da cin hanci a shekarar da ta gabata, matsalar da ta kasance karfen kafa a gwamnatin kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China