A gun taron, mataimakin sakataren kwamitin ladabtarwa da ya shugabancin taron Huang Shuxian ya jaddada cewa, kama masu cin hanci da kuma kwato kudaden da suka sata muhimman ayyuka ne wajen yaki da cin hanci, kana wata mihimmiyar hanya ce wajen hana yaduwar matsalar cin hanci da rashawa.
Hakazalika Mr Huang ya nuna cewa, aikin kama masu cin hanci a kasashen waje da kuma kwato kudaden da suka sata wani aiki ne mai sarkakkiya, wanda ke bukatar hadin gwiwa a fannonin diplomasiyya, dokoki, da hada-hadar kudi. Kamata ya yi hukumomin da abin ya shafa su bada fifikonsu, da hadin kansu don ba da gudummowa ga wannan aikin. (Zainab)