in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa sun yi maraba da sabon shafin yanar gizo na yaki da cin hanci da rashawa
2015-01-03 16:24:05 cri
Sabon shafin yaki da ayyukan da suka jibanci cin hanci da rashawa, wanda babbar hukumar yaki da cin hanci da sanya ido ta kasar Sin ta bude, na samun karbuwa a tsakanin Sinawa.

Shafin na yanar gizo wanda aka kaddamar a ranar 1 ga watan Janairun nan, na kunshe da kwafin wasikun korafi, da na koke da aka gabatarwa hukumar, tare da rahotannin yadda hukumar ta CCDI ta gudanar da bincike, game da korefe-korafen da ta karba daga dukkanin fadin kasar.

Da dama daga Sinawan da suka bayyana ra'ayoyinsu game da sabon shafin sun bayyana shi, a matsayin wata sabuwar hanyar fadada ayyukan yaki da cin hanci da rashawa a kasar. Yayin da wasu ke cewa bude shafin, waya hanya ce da za ta baiwa karin al'ummar kasar damar bada gudummawa a aikin da hukumar ke gudanarwa.

An dai tsara sabon shafin ne ta yadda Sinawa dake amfani da wayoyin kamfanin Apple, da ma sauran wayoyin hannu dake dauke da manhajar Android, za su iya aikewa da sakwannin da suka shafi cin hanci kai tsaye ga hukumar ta CCDI. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China