Wakilai fiye da dubu daya daga tawagogin kasashen da suka sa hannu kan yarjejeniyar da kungiyoyin kasa da kasa ne suke halartar taron, kuma mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Liu Zhenmin ne ya jagoranci tawagar kasar Sin.
Liu Zhenmin ya bayyana a gun taron a wannan rana cewa, kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar yaki da cin hanci, da yanke hukunci ga duk wanda ya aikata laifin cin hanci. Kana za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasa da kasa wajen yaki da cin hanci yayin da take kokarin bullo da dokoki kan wannan fanni. Ya kuma jaddada cewa, UNCAC wata dokar kasa da kasa ce dake samun karbuwa sosai a fannin cin hanci, kamata ya yi kasa da kasa su yi amfani da yarjejeniyar wajen yaki da cin hanci. (Zainab)