A yayin da hukumomin gabatar da kararraki na kasar Sin suke kokarin bin bahasin manyan laifuffuka, sun mai da hankali sosai kan laifuffukan cin hanci da karbar rashawa, wadanda suka abku a cikin ma'aikatun gwamnatin kasar. Tun daga watan Janairu zuwa Nuwamban bara, an bi bahasin irin wadannan laifuffuka guda 16510 tare da kama mutane 23017, wadanda suka lalata dukiyar kasa. Yawan kudaden da wadannan laifuffuka suka shafa ya zarce kudin Sin RMB yuan biliyan 5 da miliyan 510.
Yayin da hukumomin gabatar da kararraki na kasar Sin a matakai daban daban suke rubanya kokarinsu na bin bahasin manyan laifuffuka, su ma sun zurfafa bincike kan laifuffukan da suka shafi muhimman fannonin raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasa, da kuma lalata moriyar jama'ar kasar, sa'an nan sun yi ta kara karfinsu na kama wadanda ake tuhumarsu da laifuffukan, da kuma maido da kudaden da aka sata, sun yanke hukunci mai tsanani kan mutanen da suka aikata mabambantan laifuffukan cin hanci da karbar rashawa bisa doka yadda ya kamata. (Tasallah)