Magatakardan MDD Ban Ki-moon ya ce, yaki da cin hanci da rashawa, ya addabi duniya baki daya, saboda haka ana bukatar hada karfi domin wargaza alkadarin cin hanci a duniya.
A yayin da magatakardan na MDD ke jawabi domin tunawa da ranar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya, ya bukaci daukacin kasashe na duniya da su rattaba hannu a kan yarjejeniyar yaki da cin hanci ta MDD domin a dagargaza wannan matsala.
Ban Ki-moon ya kara da cewar, duk da yake an samu nasara a fannonin daukar cin hanci a matsayin aikata laifi, da kuma hada kan kasashen duniya wajen yaki da matsalar da gano kayayyakin da suka salwanta, to amma ya ce, har yanzu akwai jan aiki a gaba.
Ya kara da cewar, matsalar cin hanci matsala ce da ta shafi al'amurran rayuwa da harkokin siyasa da na tattalin arzikin dukanin kasashen duniya, kuma cin hancin na dakusar da damokradiyya tare da haddasa koma bayan tattalin arzikin kasa da kuma kawo tashin hankula.
Taken ranar cin hanci ta duniya na wannan shekarar shi ne "karya lagon cin hanci da rashawa", manufar bukin ranar ita ce nuna mahimmancin taka rawar jama'a wajen yaki da matsalar ta cin hanci, wace ke shafar talakawa tare da kawo cikas ga ci gaba na rayuwa saboda kudadden da ya kamata a yi amfani da su don gina kasa an kautad da su zuwa aljihun mutane. (Suwaiba)