Jiya Laraba, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta shirya wani taro tare da ministocin kasar domin samar da wani tsari a gwamnati na murkushe cin hanci da rashawa, hakan ya yi daidai da umurnin shugaban kasar Sin, Xi Jinping.
Taron wanda firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jagoranta ya samu halarcin jama'a da dama, ciki har da mataimakan firaminstan Zhang Gaoli, Liu Yandong, Wang Yang, da kuma Ma Kai.
Tun farko a Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabinsa ga wani zaman taro na babbar hukumar ladabtarwa da bincike dake karkashin jam'iyyar kwaminis, a inda ya jaddada mahimmancin yin biyayya ga dokokin jam'iyya, tare da zaburar da karin matakai na yaki da cin hanci da rashawa.
A lokacin taron, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta bayar da umurni ga hukumomin kasa da su ci kara kaimin yaki da cin hanci tare da kara daukar matakai na tabbatar da an kaucewa almubazzaranci wajen amfani da kudadden da aka kebe domin motocin gwamnati da kuma kudaden liyafa da na yin bulaguro.
A halin da ake ciki, an dauki matakai na tsarkake ababen da ke haddasa cin hanci da rashawa, a inda aka kara haske a game da nauyin bangarori dabam-dabam na gwamnati domin gudanar da ayyukan gwamnati a sarari, tare da yin kididdiga a kan kudade na gwamnati domin tabbatar da kariya kudaden jama'a
Taron ya kuma yanke shawarar ta kara gudanar da wani taron majalisar karo na 3 a kan tsarkakakkiyar gwamnati. (Suwaiba)