A lokacin shawarwarin, kasar Cuba ta kalubalanci kasar Amurka da ta fitar da ita daga jerin sunayen kasashe masu goyon bayan ta'addanci. Sai dai ita kasar Amurka ta bayyana cewa, tana yin bincike kan wannan, ta ce, bai kamata a hada wannan batu da batun farfado da dangantakar dake tsakaninsu da sake bude ofishin jakadancinsu ba. Shugabar sashen kula da harkokin kasar Amurka na ma'aikatar harkokin wajen kasar Cuba Josefina Vidal Ferreiro ta bayyana a wannan rana cewa, fitar da kasar Cuba a jerin sunayen kasashe masu goyon bayan ta'addanci ba sharadin farko na farfado da dangantakar dake tsakaninta da kasar Amurka ba ne, amma yana daya daga cikin manyan batutuwan da kasar Cuba take maid a hankali a kai.
Bayan shawarwarin, kasashen biyu sun gudanar da taron manema labaru don sanar da abubuwan da aka tattauna inda wakiliyar kasar Cuba Josefina Vidal Ferreiro ta bayyana cewa, koda yake bangarorin biyu ba su tsara lokacin gudanar da shawarwari zagaye na gaba ba, amma sun amince da kiyaye yin mu'amala da juna. Kana ta bayyana cewa, za a warware batun da ya shafi yadda ake zargin Cuba da nuna goyon baya ga ta'addanci a cikin makwanni masu zuwa. (Zainab)