in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka da Cuba sun sanar da yunkurin mayar da dangantakar dake tsakaninsu
2014-12-18 10:54:28 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama da takwaransa na Cuba Raul Castro, sun sanar da aniyar su ta gudanar da shawarwari game da mayan manufofin da suka shafi dangantakar diplomasiyyar kasashen su.

Cikin jawabin da ya gabatar a fadar White House, shugaba Obama ya ce Amurka za ta dakatar da manufofin ta game da kasar Cuba wadanda ake aiwatarwa tsawon shekaru fiye da 50, za kuma ta nemi a kaddamar da sabuwar hulda tsakanin kasashen biyu.

Ana dai sa ran cewa sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry, zai tattauna da wakilin kasar Cuba, game da batun dawo da dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu, kana kasar Amurka za ta sake gina ofishin jakadancinta a birnin Havana dake kasar ta Cuba nan da watanni masu zuwa.

Kaza lika shugaba Obama ya umarci Kerry da ya sake nazari kan kasancewar Cuba, daya daga cikin kasashen dake goyon bayan ta'addanci. Har ila yau fadar shugaban kasar Amurkan za ta yi shawarwari da majalisar dokokin kasar, game da yiwuwar soke kudurin hana hada-hadar cinikayya tsakanin Amurka da Cuba.

Bugu da kari kasar Amurkan na da fatan daukar matakan fadada cinikayya, da yawon shakatawa a tsakaninta da kasar Cuba.

A nasa bangare shugaba Raul Castro wanda ya gabatar da wani jawabi ta kafar telebijin mallakar kasar sa, ya ce ya tattauna da shugaba Obama ta wayar tarho a ranar 16 ga watan nan, sun kuma amince da daukar matakai bisa ka'idojin kasa da kasa, da tsarin dokokin MDD, don sake kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu yadda ya kamata.

Sakamakon cimma wannan nasara ne ma kasashen biyu suka fara daukar wasu matakan kyautata dangantaka a wannan rana, ciki hadda sakin wani dan kasuwar kasar Amurka Alan Gross da mahukuntan Cuba suka yi, bayan ya shafe shekaru 5 a tsare, da kuma wani dan leken asirin Amurka da aka tsare a Cuban tsawon shekaru 20.

A nata bangare Amurka ta saki 'yan leken asirin kasar Cuba su 3, wadanda take tsare da su tsawon shekaru 15. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China