in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya isa Havana don fara ziyarar aiki
2014-07-22 11:03:27 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Havana na kasar Cuba don gudanar da ziyarar aiki a karon farko tun lokacin da ya kama aiki a matsayin shugaban kasar Sin.

Yayin da yake kasar ta Cuba, ana sa ran shugaba Xi zai tattauna da shugaba Raul Castro, inda za su tsara wata taswirar bunkasa dangantaka tsakanin kasashen biyu bisa manya tsare-tsare cikin dogon lokaci.

Bugu da kari sassan biyu za su sanya hannu kan takardun hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki, cinikayya, aikin gona, fasahar kere-kere ta fuskar tsirrai, al'adu da kuma ilimi.

Kasar Cuba ita ce zangon karshe na rangadin da shugaba Xi ke yi a kasashen Latin Amurka, ziyarar da tuni ta kai shi kasar Brzail inda ya halarci taron kasashen kungiyar BRICS, kana daga bisani ya ziyarci kasashen Argentina da Venezuela. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China