in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan kasar Sin ya yi kira da a kiyaye tsarin duniya na kayyade makamai da hana yaduwar makaman kare dangi bayan yakin duniya na 2
2015-03-10 16:50:35 cri

A jiya Litinin 9 ga wata Fu Cong, sabon jakadan kasar Sin mai kula da batun kwance damara, ya yi kira ga kasashen duniya da su hada kai wajen kiyaye tsarin kasa da kasa, game da kayyade makamai, da hana yaduwar makaman kare dangi bayan yakin duniya na 2, sa'an nan su dauki matakan diplomasiyya na yin rigakafin abkuwar hargitsi bisa sabon tunani ta fuskar tsaro. Ya ce ya kamata a kara azama a fagen ayyukan kayyade makamai a duniya, a kokarin sa kaimi ga manufar wanzar da zaman lafiya a duniya baki daya.

Mista Fu Cong ya bayyana hakan ne a yayin shawarwarin da aka gudanar a birnin Geneva game da batun kwance damara. Ya kara da cewa, shekarar bana, shekara ce ta cika shekaru 70 da kafuwar Majalisar Dinkin Duniya, da kuma samun nasarar yaki da 'yan Nazi a duniya. Kiyaye tsarin kasa da kasa kan tsaro da aka kafa bayan babban yakin duniya na 2, ya dace da moriyar yawancin kasashen duniya. Har wa yau kuma "yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya", da "yarjejeniyar hana amfani da makamai masu guba", da "yarjejeniyar hana makamai da ake yi daga kwayoyin halittu masu rai", da "yarjejeniyar hana gwaje-gwajen makaman nukiliya daga dukkan fannoni" da sauran yarjejeniyoyin da aka daddale a tsakanin bangarori 2, ko bangarori daban daban dangane da kayyade makamai da kuma kwance damara, dukkanin su sun kasance tamkar ginshiki na tabbatar da tsarin kasa da kasa kan tsaro, bayan kammalar babban yakin duniya na 2, wadanda kuma suka taka muhimmiyar rawa.

A halin yanzu, kamata ya yi a kara sauke nauyi yadda ya kamata, a cika alkawarin da aka tanada cikin yarjejeniyoyin, a kiyaye mutunci da martabar tsarin duniya game da kayyade makamai, da hana yaduwar makaman kare dangi, a taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman lafiya da tsaro a dukkanin duniya.

Haka zalika, Fu Cong ya bayyana cewa, a 'yan kwanakin baya, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da sabon tunani na bai daya, kuma tunani mai dorewa kan batun tsaro da ke bukatar hadin gwiwar kasa da kasa. Wannan sabon tunani ya samar da jagoranci, da kuma sa kaimi kan kokarin kayyade makamai a duniya.

Ba za a iya samun tsaro na gaskiya kuma mai dorewa ba, har sai an samu tsaro a dukkanin sassan duniya. Kuma bai kamata wata kasa ta tabbatar da tsaron kanta ta hanyar da za ta haifar da rashin tsaro a sauran kasashe ba. Daukar irin wannan mataki zai sa ayyukan kayyade makamai, da hana yaduwar makaman kare dangi da ake gudanarwa a duniya ya gaza samun goyon baya daga kasashen duniya, kuma ba za a iya gudanar da su yadda ya kamata ba.

Bayan haka, mista Fu ya gabatar da sabuwar shawara dangane da yadda za a bunkasa shawarwari kan kwance damara, da kuma kara azama kan ayyukan kayyade makamai a duniya. A cewarsa bunkasuwar kimiyya da fasaha na kawo wa dan Adam alheri da dimbin zarafi, a sa'i daya kuma, yin amfani da su a fannin aikin soja, kan haddasa babbar barazana ga tsaron lafiyar dan Adam, da ma wanzuwar dan Adam a duniya. Saboda haka kamata ya yi a himmantu wajen daukar matakan diplomasiyya na rigakafin abkuwar tashe tashen hankula, a yi iyakacin kokarin hana takarar makamai da ake amfani da su a sararin samaniya da kuma Intanet.

Har ila yau, in ji jakadan, game da zummar farfado da shawarwarin Geneva kan kwance damara, batun dake da muhimmanci shi ne sarrafa lokacin da ake da shi yadda ya dace, da kuma yin amfani da tunani da kaifin basira bisa sabon halin da ake ciki.

Da farko kamata ya yi a inganta wakilcin shawarwarin, wato a kara shigar da kasashe cikin shawarwarin. Na biyu ya kamata a tattauna sabbin batutuwa da suka jibanci shawarwarin, kamar tabbatar da tsaron bayanai, da hana takarar makamai a intanet da dai sauransu. Na uku kamata ya yi a tsara ka'idoji kan barazanar tsaro da ake fuskanta a duniya a zahiri, da sauran batutuwan da ke jawo hankalin kasa da kasa.

Yanzu haka dai kasashe 65 suna cikin mambobin shirin shawarwarin Geneva kan batun kwance damara, wanda ya zamo dandali daya tilo a duniya, na yin shawarwari tsakanin sassa daban daban kan batun kwance damara, inda a baya ta hanyar yin shawarwarin ne aka daddale wasu muhimman yarjejeniyoyi na kayyade makamai tsakanin sassa daban daban, kamar"yarjejeniyar hana gwaje-gwajen makaman nukiliya daga dukkan fannoni". (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China