Babban daraktan hukuma mai yaki da makamai masu guba Ahmet Uzumcu, ya bayyana kammala aikin debe daukacin sinadarai masu guda daga kasar Sham, a matsayin wani muhimmin mataki da ya cancanci yabo.
An dai yi jigilar kashin karshe na irin wadannan sinadarai ne daga kasar ta Syria a ranar Litinin, kamar yadda wata sanarwa da hukumar ta OPCW ta fitar. Wannan kuma ya kasance sakamako dake shaida kammalar bangaren lalata wadannan sinadarai mafi muhimmaci da OPCW za ta yi.
A cikin watan Oktobar bara ne dai OPCW ta fara aikin fidda sinadarai masu guba daga Syria, karkashin shirin lalata su da ake fatan aiwatarwa a nan gaba.
A wani ci gaban kuma, ma'aikatar wajen kasar Rasha ta yi maraba da kammalar wannan aiki na jigilar sinadarai masu hadari daga Syria, tana mai bayyana hakan a matsayin aiki mai tattare da gagarumar nasara. (Saminu)