Mahukunta kasar Amurka sun bayyana aniyyarsu ta ci gaba da samar da makamai ga kasar Iraki, inda a wannan watan kadai ta samar kasar makamai masu linzami guda 100 da dubban daruruwan albarusai.
Ofishin jakadancin kasar Amurka da ke Bagadaza, babban birnin kasar Iraki shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa. Ya ce, wannan wani mataki ne na samar wa dakarun tsaron kasar ta Iraki makamai na zamani, ta yadda za su tunkari kalubalen tsaro da kasar da kuma shiyyar ke fuskanta.
A cewar sanarwar, tun daga tsakiyar watan Janairun wannan shekara, kasar ta amurka ta samar wa dakarun tsaron kasar (ISF) sama da albarusai miliyan 11 da dubban bindigogi da gurneti da sauran muhimman makaman da ake bukata, ofishin jakadancin Amurka ya ce, yana duba yiwuwar aiki tare da shugabanni da kwamamdojin sojan kasar, ta yadda za su magance karin matsalar makaman da suka bukata a cikin 'yan makonni masu zuwa.
Alkaluman MDD na nuna cewa, kimanin 'yan Iraki 8,868, ciki har da fararen hula 7,818 da jami'an 'yan sanda ne aka kashe a shekarar 2013, adadi mafi yawa a cikin wadannan shekaru. (Ibrahim)