Sanarwar ta ce, mai shiga tsakani na musamman na kungiyar OPCW ya nuna a wannan rana cewa, za a jinkirta aikin jigilar makamai masu guba a karo na farko daga Syria bisa ga shirin da aka tsara, tare da bayyana cewa za a kammala shi kafin ranar 31 ga wata a sakamakon wasu dalilai. Amma Ban Ki-moon ya jaddada cewa, kokarin kasashen duniya na kawar da makamai masu guba na Syria na samun ci gaba a ko da yaushe, cikin watanni uku da suka wuce, an cimma dukkan muhimman ayyukan a wannan fanni yadda ya kamata. (Fatima)