A ranar Labara 5 ga watan nan na Maris ne kwamitin tsaron MDD ya amince da wani kuduri na tsawaita wa'adin dokar nan, da ta tanaji haramta shigar da makamai masu hadari Somaliya har ya zuwa watanni 8 masu zuwa.
Wannan kuduri dai ya jaddada kira ga daukacin kasashe mambobin kwamitin na tsaro, da su kauracewa karya wannan doka, domin kaucewa fadawar makamai hannayen 'yan tada kayar baya, dake yunkurin wargaza shirin wanzar da zaman lafiya a kasar.
Kudurin ya kuma yi Allah wadai da kwararar makamai cikin kasar ba bisa ka'ida ba, matakin da aka bayyana a matsayin yiwa dokar kwamitin tsaron karan tsaye.
A watam Maris na shekrar da ta shude ne dai kwamitin, ya dage wani sashen na waccan doka da aka shafi shekaru 21 ana aiwatarwa a kasar, domin baiwa mahukuntan kasar damar mallakar kananan makamai, a matsayin wani mataki na fuskantar kalubalen kungiyar 'yan kaifin kishin Islama ta Al-Shabaab.
An dai kafa wannan doka ne a shekarar 1992, domin dakile tasirin da kwararar makamai ke haifarwa, wajen rura wutar rikicin da ya dade yana addabar kasar ta Somaliya. (Saminu)