Wata tawaga mai kunshe da sojojin Amurka da kwararru kan lalata makamai masu guba sun fara aikin lalata sinadarai masu guba na kasar Syria.
Kakakin ma'aikatar tsaron Amurka Steve Warren ya shaidawa manema labarai cewa, jirgin ruwan Amurka mai suna MV Cape Ray, ya bar Gioia Tauro na kasar Italiya dauke da tan 600 na sinadarai masu guba na kasar ta Syria, inda ake sa ran za a lalata su a ruwayen kasa da kasa.
Idan har komai ya tafi kamar yadda aka tsara, za a dauki kwanaki 60 ne ana gudanar da wannan aikin, sai dai akwai fargabar matsalar yanayi tana iya kawo cikas ga aikin. (Ibrahim)