Hong ya ce, a bayyane yake cewa Sin tana tsayawa tsayin daka kan matsayin da ta dauka dangane da makamai masu guba. Sin ba za ta amince ma kowa ba wajen amfani da su, kuma da babbar murya ta yi Allah wadai da wadanda suka taba amfani da makamai masu guba a Syria. Ya jaddada cewa, Sin tana goyon bayan rukunin MDD wajen ci gaba da aikinsa bisa yarjejeniya tsakaninsa da gwamnatin Syria. Kuma Sin na maraba da yarjejeniyar da Amurka da Rasha suka daddale, da nuna goyon baya ga soma aikin lalata makamai masu guba na Syria karkashin kulawar MDD, tare da sa kaimi ga yunkurin daidaita batun a siyasance.(Fatima)