Bisa labarin da aka gabatar, an ce, a cikin wannan wasika, ma'aikatar harkokin waje ta Syria ta yi zargi kan wasu kasashe da cewa, ba su kimanta kokarin kasar na tabbatar da yarjejeniyar hana bazuwar makamai masu guba yadda ya kamata ba, kuma ta yi kira ga kasashen duniya da su fuskanci hadarin da za a gamu da shi yayin da ake kokarin lalata makamai masu guba, wadanda suka hada da munanan ayyuka da 'yan adawa suka aikata.
A cikin wannan sako, ma'aikatar harkokin waje ta Syria ta kara da cewa, nan ba da dadewa ba gwamnatin Syria za ta yi jigilar makamai masu guba da yawa, amma kafin wannan dole ne a daidaita wasu matsaloli bayan yin shawarwari da MDD da kungiyar hana bazuwar makamai masu guba.
Bisa shirin lalata makamai masu guba na Syria da kungiyar hana bazuwar makamai masu guba ta fitar a watan Nuwamba na bara, kamata ya yi a yi jigilar makaman a karon farko kafin karshen bara. Amma har zuwa farkon shekarar bana, aka fara wannan aiki. Bugu da kari, an ce kamata ya yi a yi jigilar duk makamai masu guba daga Syria zuwa ketare domin lalata su kafin ranar 5 ga wata, amma har zuwa yanzu, kashi 5 cikin 100 kawai aka yi jigilarsu daga Syria zuwa ketare.(Fatima)