Mahukunta a kasar Burundi sun yi kira ga MDD, da ta gudanar da zuzzurfan bincike, game da zargin da akewa gwamnatin kasar mai ci, na rabawa matasan dake goyon bayan jam'iyya mai mulki makamai.
Hakan, a cewar mai magana da yawun gwamnatin kasar Philippe Nzobonariba, ya zama wajibi domin zai wanke gwamnatin mai ci daga wancan zargi, tare da kwantar da hankulan sassan da batun ya shafa.
Tun da fari dai babbar jam'iyyar adawar kasar wato "Democrats' Alliance for Change" ce, ta zargi babbar jam'iyya mai mulki ta CNDD-FDD, da rabawa reshen matasanta da akewa lakabi da Imbonerakure makamai, lamarin da 'yan adawar ke cewa, zai iya jefa kasar cikin wani mawuyacin halin rashin tabbas, musamman ma a wannan gaba da babban zaben kasar na badi ke dada karatowa.
Gudanar da bincike ne kadai, a cewar Philippe Nzobonariba, zai wanke gwamnatin Burundi daga wannan zargi, wanda tuni 'yan adawar suka mika shi ga ofishin babban magatakardar MDD. Ko da yake dai mahukuntan jam'iyyar, da tsagin gwamnati sun yi watsi da shi, tare da bayyana shi a matsayin zargi maras tushe ko makama. (Saminu)