Kakakin babban taro na 3 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 12 Fu ying, ta ce kasar Sin na duba yiwuwar amfani da karin ka'idojin hukunta laifuffuka ta kasa da kasa, don nuna cikakken amfanin doka, da tsari na kasa da kasa, ta yadda za a sanya jami'ai masu cin hanci da rashawa fuskantar hukunci ko ina suka gudu.
Madam Fu ta ce, yanzu ana samun masu aikata laifin cin hanci da rashawa da yawa a kasar Sin, hakan na nufin ya dade ana samun matsala a wannan fanni, don haka dole ne a dauki matakai masu tsanani wajen yaki da cin hanci da rashawa. Haka kuma, a bangaren zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya kamata a karfafa tsarin yaki da cin hanci da rashawa, domin kafa wani yanayin da zai dakile yaduwar irin wadannan laifuffuka. (Lami)