An ce, akwai ginshikai uku a cikin shirye-shiryen da aka gabatar a bana. Na farko shi ne gudanar da ayyuka a dukkan fannoni bisa tunanin da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis na Sin ya gabatar. Inda aka nuna cewa ya kamata mambobin majalisar su gabatar da shawarwari da ra'ayoyi kan sabon tsarin yau da kullum kan tattalin arziki da yadda za a kiyaye bunkasuwar tattalin arziki ba tare da tangarda ba da dai sauransu.
Na biyu shi ne gabatar da ra'ayoyi game da zurfafa kwaskwarima, da gudanar da ayyukan kasar bisa dokoki.
Na uku kuma shi ne bada shawara kan batun kyautata zaman rayuwar jama'a, da bada tabbaci ga zamantakewar al'ummar kasar, da kuma gabatar da ra'ayoyi a fannonin bada ilimi, da kiwon lafiya, da ciyar da tsofaffi, da kiyaye muhalli da jama'ar kasar ke maida hankali matuka a kansu. (Zainab)