Shugaban majalisar Yu Zhengsheng wanda ya bayyana hakan yau lokacin da yake gabatar da rahoton aikin kwamitin hukumar a taronta na shekara-shekara ya ce, majalisar za ta mayar da hankali kan batutuwa guda hudu yayin take gudanar da ayyukanta.
Ya ce, wadannan muhimman batutuwa su ne batutuwan da shugaba Xi Jinping ya gabatar wadanda suka hada da gina al'umma mai annashuwa da wadata, tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa dokoki, zurfafa yin gyare-gyare da kuma tafiyar da harkokin jam'iyya bisa doka.
Yu ya ce, shekarar ta 2015 shekara ce mai sarkakiya ga shirin zurfafa yin gyare-gyare, kuma shekara ce da aka kara zurfafa tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka daga dukkan fannoni, kana shekara ce ta karshe ta kammala karo na 12 na ayyukan da aka tsara gudanarwa cikin shekaru biyar.
Don haka ya ce, kamata ya yi majalisar ta mayar da hankali kan shawarwarin da aka gabatar game da gyare-gyare da sauran ayyukanta da suka shafi ci gaban kasa a shekarar da ta gabata tare da tsara sabbin manufofin da ake son cimmawa a shekara 2015. (Ibrahim Yaya)