Da safiyar Larabar nan ne aka bude zaman share fagen taro na 3, na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 12, a babban dakin taron jama'ar kasar Sin.
Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang shi ne ya bude taron, inda aka zabi tawagar shugabanni, da sakataren taron, aka kuma sanar da ajandar taron.
Mr. Zhang ya sanar a gun taron cewa, za a bude taro na 3 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a ranar 5 ga wata, kuma an riga an kammala aikin shirya taron.
Bisa ajandar taron da aka gabatar, wakilan jama'ar kasar Sin za su duba rahoton ayyukan gwamnatin kasa, za kuma su yi nazari kan aikin gudanar da shirin tattalin arziki da bunkasuwar al'umma na shekarar 2014, da kuma zartas da shirin da aka gabatar na shekarar 2015.
Ban da haka kuma, za a nazarci yadda ake aiwatar da kasafin kudi na gwamnatin tsakiya, da na gwamnatocin matakai daban daban na shekarar 2014, da zartas da kasafin kudi na shekarar 2015. Kazalika, za a tattauna kan daftarin dokar tsara dokoki, sannan za a saurari, tare da bincike kan rahoton aiki da zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'a ya gabatar, da rahoton aiki na babbar kotu, da kuma rahoton aiki na babbar hukumar gabatar da kara ta kasar Sin.(Lami)