A yau da yamma ne aka gudanar da taron manema labau kan cikakken zama na shekara-shekara, na majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin karo 12 a nan birnin Beijing, inda Lv Xinhua ya ce, a farkon lokacin bude kofa ga waje, akwai masallatai kimanin dubu 2 a yanki mai cin gashin kansa na Uygur na jihar Xinjiang ta Sin, amma ya zuwa yanzu, ana da masallatai sama da dubu 20 a jihar, kana adadin ma'aikatan masallatan ya karu daga dubu 3 zuwa dubu 28. Kaza lika, tun farkon shekarar 2001 har zuwa yanzu, gaba daya gwamnatin jihar ta aike da mutane 47 zuwa wasu manyan jami'o'in Musulunci dake kasashen Masar, Pakistan da dai sauransu domin karo ilimi. Kana gaba daya an fitar da litattafai da mujallolin Musulunci na harshen Uygur kimanin miliyan 1 a jihar. (Maryam)