in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutanen da suka bace sakamakon hadarin jiragen ruwa a tekun Bahar Rum sun zarta 300
2015-02-12 14:49:44 cri

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR ta ba da labari a ran 11 ga wata, inda ta tabbatar da cewa, jiragen ruwa guda hudu dauke da mutanen dake kokarin ketarawa zuwa Italiya ba bisa doka ba sun nutse cikin tekun, kuma ana ganin mutanen da suka bace ya kai fiye da 300.

Hukumar ta bada wata sanarwa a ran 10 ga wata inda ta ce, mutane 29 dake kokarin shiga turai suka rasa rayukansu a sararin tekun tsibirin lampedusa na Italiya kan hanyarsu ta ratsa ruwan Bahar Rum. Kuma bisa nazarin da 'yan sandan Italiya suka yi, hukumar ta bayyana a ran 11 ga wata cewa, mutane kimanin 300 sun bace.

Yawancin wadannan mutane sun fito daga kasashen Afrika dake kudu da Sahara, inda suka dauko jiragen ruwa hudu tun daga Libya zuwa Italiya.

Wasu daga cikin wadanda suka tsirar da ransu sun shedawa hukumar cewa, jirgin ruwan da suka shiga ya tashi daga Libya a ran Asabar da ta shude tare da shafe kwanaki da dama cikin teku, babu ruwan sha kuma babu abinci.

A halin yanzu dai 'yan sandan Italiya na ci gaba da gano wadanda suka bace, duk da matsalar yanayi mai tsanani da suke fuskanta. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China