Shugabar kasar Koriya ta Kudu Park Geun-hye a Litinin din nan ta sake neman gafara a hukumance game da hadarin jirgin ruwa da ya faru a watan jiya wanda shi ne mafi muni a tarihin baya bayan nan, tana mai daukar alwashin yin kwaskwarima game da ayyukan samar da ceton gaggawa.
Madam Park ya zuwa yanzu ta nemi gafara sau hudu ke nan tun faruwar hadarin jirgin ruwan mai nauyin tan 6,825 da ya kife tare da nutsewa a kudu maso yammacin tsibirin Jindo a ranar 16 ga watan Afrilu, sai dai wannan ne karo na farko da ta nemi gafara a madadin gwamnati cikin wata sanarwa a hukumance.
A ranar ta 34 da faruwar hadarin da kuma fara neman wadanda suka bata, an tabbatar da mutuwar mutane 286, har yanzu kuma ana kan neman mutane 18, ba wanda aka samu da rai tun bayan mutane 172 da aka ceto su jim kadan da kifewar jirgin.
Shugaba Park ta ce, masu aikin ceto na jirgin ruwan ba su yi wani hobbasa ba a lokacin da jirgin ya kife, don haka bayan nazari mai zurfi ta tsai da shawarar rusa wannan ofishi. (Fatimah)