Kasar Aljeriya ta tabbatar a ranar Alhamis cewa, jirgin saman fasinja mai lambar AH5017 na kamfanin sufurin jiragen saman Aljeriya ya fadi a kasar Mali tare da fasinja 116, in ji kafofin watsa labarai na kasar.
Muna iyar tabbatar da cewa, jirgin saman ya fadi a cikin kasar Mali, kana akwai ma'aikatan agaji da suka kusanci wurin da jirgin ya fadi, in ji ministan harkokin wajen kasar Aljeriya, Ramtane Lamamra, da kamfanin dillancin labaran Aljeriya APS ya rawaito kalamansa.
Mista Lamamra ya yi wannan furucin a yayin taron manema labarai a birnin Alger, bayan rattaba hannu kan jadawalin tattauna batun zaman lafiya tsakanin gwamnatin Mali da gungun 'yan tawaye dake yankin arewacin kasar Mali.
Jami'in ya cigaba da cewa, jirgin saman na dauke da fasinjoji 'yan asilin kasashe goma sha uku, ba tare da ba da wani karin haske ba.
Kamfanin Air Algeria ya sanar cewa, jirgin saman, samfurin MD-83 na kamfanin Swift Air na kasar Spaniya dake bisa hanyar Ouagadougou zuwa Alger, ya bace mintoci hamsin bayan tashinsa. (Maman Ada)