A yayin da ake ci gaba da kai daukan mataki na fito da wadanda hadarin jirgin ruwan Koriya ta Kudu ya rutsa da su, bayan da jirgin ruwan ya nutse cikin ruwa, adadin wadanda suka mutu, ya karu zuwa mutane 104.
A daidai karfe 10 na safiyan yau, agogon kasar, an tabbatar da rasuwar mutane 104, a inda kuma wasu mutane 198, kawo ya zuwa yanzu, ba'a san inda suke ba. Hakazalika yanzu an ceto mutane 174. Aikin ceton da aka shafe dare ana yi ya haifar da gano gawawwaki fiye da goma.
Gwanayen masu nutso a cikin ruwa, sun fara shiga cikin ruwan tare da neman jirgin da ya nutse tun daga ranar Litinin, to amma hakan sai ya yi sanadiyyar karin adadin wadanda suka rasa rayukansu. A ranar Litinin kawai an gano gawawwaki 28.
Har yanzu dai babu rahotannin alamun yiwuwar sake samun fasinjoji da rai. (Suwaiba)