Mardjono Siswosumarno ya ce bisa amfani da wasu nau'rorin musamman sun hango akwati baki na 2 wanda ya kasance rakodar nadir bayanai na jirgin Air Asia wanda ya fadi a kwanan nan.
Masu nutso daga kasar Indonesia a safiyar yau sun gano rakodar jirgin daga cikin tekun Java.
Kokarin da ake yi na samar da bayanai da kuma rakodar direban jirgin saman yana da gagarumin tasiri wajen gano musabbabin hadarin jirgin saman.
Sai dai kuma binciken farko sun nuna cewa hadarin da jirgin saman ya yi yana da nasaba da rashin kyawon yanayi.(Suwaiba)