in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadarin mota ya kashe mutane 56 a Sudan ta Kudu
2014-09-30 09:36:13 cri

A kalla mutane 56 aka tabbatar sun mutu a ranar Litinin a wani taho-mu-gama tsakanin wata karamar motar fasinja da wata motar daukon kaya a kan hanyar Sudan ta Kudu dake zuwa kasar Uganda, a cewar wata majiya ta asbitin Djouba.

Akwai yiyuwar adadin mutanen da hadarin ya rutsa da su ya karu, amma wadanda aka kawo asibiti su 56 ne, in ji wannan majiya da ta nemi a boye sunanta. Ana samun zirga-zirgar motoci sosai a kan hanyar dake hada Sudan ta Kudu da sauran kasashe makwabtanta tun lokacin da tashe-tashen hankalin da suka barka a cikin watan Satumban da ya gabata tsakanin sojojin gwamnatin kasar da mayakan dake goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu, Riek Machar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China