Mutane fiye da 30 ne suka mutu, yayin da 79 suka jikkata a lokacin da jirgin kasan kamfanin layin dogo na jamhuriyar demokuradiyar kasar Congo DRC (SNCC) ya fita daga hanyarsa a ranar Talata a gundumar Katanga dake kudu maso gabashin kasar DRC-Congo, in ji wani jami'in kamfanin SNCC.
Hadarin ya faru a kusa da gadar Katongola, kusan kilomita 50 da Kimina, kimanin kilomita 270 daga arewa maso yammacin Lubumbashi.
Jami'in na SNCC ya nuna cewa, gudun wuce hankali ne zai kasance babban dalilin wannan hadari. Wani fasinja na jirgin kasan ya ce, jirgin ya nade kafin ya fita daga hanyarsa. (Maman Ada)