in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya yi kira kan samun ci gaba tare
2015-01-20 11:25:24 cri
A jiya ne, kwamitin sulhu na MDD ya bukaci da a tsara wani shiri domin inganta ayyukan neman ci gaba tare, ta yadda za a iya yin rigakafin abkuwar rikice-rikice da kuma cimma burin samun dauwamammen zaman lafiya.

A wannan rana, kwamitin sulhu na MDD ya gudanar da shawarwari a bainar jama'a kan samun ci gaba tare, kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya, an kuma zartas da wata sanarwar shugaba, inda aka nuna cewa, tsaro da bunkasuwa manyan batutuwa ne na samun dauwamammen ci gaba, kuma ba za a cimma wannan buri ba, muddin bangarorin da abin ya shafa ba su shiga an dama da su a wannan aiki ba

Cikin sanarwar, an nuna cewa, neman ci gaba tare wani muhimmin aiki ne ga yin rigakafin abkuwar rikice-rikice, sannan samun zaman kafiya da kwanciyar hankali na dogon lokaci, ya sa kaimi ga mambobin MDD su tsara wani shirin hadin gwiwa na MDD domin inganta ayyukan neman ci gaba tare. Kwamitin sulhu na MDD ya kuma bukaci mambobin MDD da su tsara shirin tare da bangarorin da abin ya shafa, ciki hada da yin shawarwari kan batutuwan da suka shafi addini, kabilu da na al'adu, kawar da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi, da kuma kawar da yaduwar rikice-rikice. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China