Wang Min ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar, yayin taron kwamitin sulhu kan batun sanya takunkumi a kokarin tinkarar wasu matsaloli. Mr. Wang ya ce kamata ya yi kwamitin sulhun ya yi amfani da hanyoyin sulhutawa, da na shiga-tsakani, da tattaunawa, tare da bin hanyoyin da ba na karfin tuwo ba, da ma bin ka'idojin tsarin mulkin MDD da kuma dokokin kasa da kasa.
Kaza lika a cewar wakilin kasar ta Sin, kasar sa ba za ta amince da duk wani mataki na kakaba takunkumi ga sauran kasashe bisa dokar da wata kasa ke amfani da ita a gidanta ba.
Wang Min ya ce, a matsayin kasa mai kujerar dindindin a kwamitin na sulhu, kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan yin takatsantsan, da daukar nauyin warware matsaloli, da sa kaimi ga kwamitin sulhu wajen kara inganta aikin sanya takunkumi, da kara kwazo na warware matsaloli ta hanyar siyasa.
Kana kasar Sin tana fatan hada gwiwa da membobin kwamitin sulhu, da kasashe membobin MDD wajen sa kaimi ga kwamitin sulhun MDD, wajen sauke nauyin dake wuyan ta, da bada gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro masu dorewa a duniya. (Zainab)