Mr. Liu ya bayyana hakan ne yayin taron kwamitin sulhun MDD kan hadin gwiwa da kungiyar ta AU a fannin kiyaye zaman lafiya, wanda ya gudana a ranar 16 ga watan nan.
Ya ce kungiyar AU ce ke da bayanai da dabarun yadda za a warware matsaloli a yankunanta, bisa la'akari da matsayin kasashen na Afirka, da shirye-shiryen da ake da su na warware matsalolin nahiyar. Don haka kamata ya yi kwamitin sulhun MDDr ya yi la'akari tare da nuna goyon baya ga kungiyar ta AU, a kokarin shawo kan matsalolin dake haddasa rikice-rikice, da sauraron ra'ayoyi, da shawarwari daga kungiyar ta AU. (Zainab)