A wannan rana da dare, cibiyar ba da jagoranci ta 'yan sandan kwantar da tarzoma ta kasar Sin ta samu rahoton cewa, an ga hayaki na tashi a yammacin runbun adana man na UNMIL, wanda kuma ke yaduwa zuwa sauran na'urorin ajiyar man. Nan da nan cibiyar ta aika da 'yan sanda da motar kashe gobara zuwa wurin inda suka kwashe mintoci sama da 40 kafin su kashe wutar, sannan nan babu na'urorin da suka lalace.
Bayanai na cewa, wutar ta tashi ne yayin da wasu mazauna da ke kusa da defon adana man ke dafa abinci.
Wani jami'i a defon ya nuna godiya ga daukin gaggawa da 'yan sandan kwantar da tarzoma na kasar Sin suka ba da kwarewarsu da kuma jarunkarsu wadda ta taimaka wajen ceto MDD daga fusakantar wata babbar hasarar. (Bilkisu)