in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya yi kira da a ci gaba da kokarin kiyaye hakkin yara
2014-11-21 10:26:35 cri

Ranar 20 ga wata ranar yara ce ta duniya. A wannan rana, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi jawabi domin yin kira da a ci gaba da kokarin kiyaye ikon yara yayin da ake murnar cika shekaru 25 da zartas da yarjejeniyar kare hakkin yara.

A cikin jawabinsa, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, kowane yaro na da ikon girma lami lafiya, da samun ilmi, da kauracewa azaba, da kuma bayar da ra'ayinsa. Kafin shekaru 25, MDD ta zartas da yarjejeniyar kare hakkin yara. Ya zuwa yanzu, kusan kowace kasa a duniya ta zartas da wannan yarjejeniya. A kasashen duniya, yarjejeniyar ta tilasta wa mutane kyautata dokoki da manufofi a wannan fanni, da canza hanyar aikinmu ta sa kaimi ga kiyaye ikon yara.

Ban Ki-moon ya kara da cewa, kamata ya yi a yi kokarin sa kaimi ga kare hakkin yara, musammun ma yaran da ba su samun kulawa sosai, amma kuma suna bukatar taimako kwarai.

Ban Ki-moon ya yi kira da a hada gwiwa domin ba da kariya ga ikon yara a duniya, da zummar kafa wata duniya mafi adalci, a kokarin samar da makoma mai kyau ga duk bil'adam.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China