Bisa kudurin, ana fatan za a kara ingancin ayyukan 'yan sanda na MDD, da tsara da aiwatar da ayyukan bisa ka'idoji na tsarin jagorancin ayyukan tabbatar da zaman lafiya da 'yan sanda na kasa da kasa suke yi. Kana kudurin ya kalubalanci kasa da kasa da suka taba tura 'yan sanda da su ci gaba da tura 'yan sanda masu fasahohi da kammala ayyukan tawagogin musamman na MDD. Haka kuma kudurin ya sa kaimi ga kasashen da hukumomin MDD da abin ya shafa da su samar da horaswa ga dukkan 'yan sanda don taimaka musu wajen daukar alhakinsu kan tabbatar da zaman lafiya da bada kariya ga kananan yara.
Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wang Min ya bayyana a wannan ranar ta Alhamis 20 ga wata cewa, kamata ya yi MDD ta kara nuna goyon baya da horar da 'yan sandan kiyaye zaman lafiya na kungiyar AU da na sauran kungiyoyin yankuna don taimaka musu wajen kara taka muhimmiyar rawa kan tabbatar da zaman lafiya da na karko a yankinsu. Ya ce kasar Sin tana son yin kokari tare da kasa da kasa wajen bada gudummawa kan sa kaimi ga samun bunkasuwa mai dorewa kan aikin 'yan sanda na MDD da kuma tabbatar da zaman lafiya a fadin duniya. (Zainab)