in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi babban taron MDD ya duba batutuwan samun bunkasuwa da kasashe masu tasowa suke sa lura kansu
2014-11-19 15:35:39 cri
Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Wang Min ya bayyana a cibiyar MDD dake birnin New York a ranar 18 ga wata cewa, kamata ya yi babban taron MDD ya duba manyan batutuwan dake shafar moriyar kasashe membobin kungiyar, musamman ma batutuwan samun bunkasuwa da kasashe masu tasowa suke sa lura kansu.

Wang Min ya bayyana haka a gun babban zaman taron da MDD ta gudanar a wannan rana, inda ya ce kamata ya yi babban taron MDD ya yi amfani da ikonsa na duba manufofi don sa kaimi ga kasashe membobin kungiyar da su shiga ayyukan kungiyar. Kana ya kamata babban taron MDD ya tabbatar da wane irin aiki ne da za a gudanar da farko bisa halin da ake ciki a duniya, da tattauna da tinkarar manyan batutuwan dake shafar moriyar kasashe membobin kungiyar, musamman ma batutuwan samun bunkasuwa da kasashe masu tasowa suke sa lura kansu. Ya kamata, babban taron MDD a wannan karo ya kara maida hankali kan batun samun bunkasuwa, da taka muhimmiyar rawa kan tsara ajandan samun bunkasuwa bayan shakarar 2015, da sa kaimi ga samun bunkasuwa mai dorewa.

Ban da wannan kuma, Wang Min ya bayyana cewa, ya kamata babban taron MDD da kwamitin sulhu na MDD da sauran hukumomin MDD su kara yin hadin gwiwa, da ci gaba da yin amfani da fifikonsu, da kuma kara yin mu'amala da juna. A fannin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, ya kamata babban taron MDD ya raba ayyuka bisa kundin tsarin mulkin majalisar da kara yin hadin gwiwa a tsakaninsa da kwamitin sulhu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China