in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakiyar babban sakataren MDD ta yi murabus
2014-11-27 14:26:45 cri
A jiya Laraba ne mataimakiyar babban sakataren MDD mai kula da harkokin jin kai Madam Valerie Amos, ta gabatar da takardar murabus ga babban magatakardan MDD Ban Ki-moon.

A cewar kakakin babban magatakardan MDD Farhan Haq, Amos wadda ta kasance a wannan matsayin tsawon shekaru hudu, za ta sauka daga mukamin nata ne a watan Maris na shekarar mai zuwa.

Farhan Haq ya kuma gabatar da sanarwar da Ban Ki-moon ya fitar game da wannan batu, sanarwar da baya ga amincewa da murabus din nata, ya kuma bayyana godiyarsa game da irin gudummawar da Amos ta bayar ga kungiyoyin jin kai, da masu bukatar ayyukan jin kan. Ko da yake dai ba a bayyana dalilin da ya sanya jami'ar yin murabus a yanzu ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China