Cikin wata sanarwar da kwamitin sulhu na MDD ya fitar, kwamitin ya nuna takaicinsa, ganin yadda rundunar ta AMISOM da ta dade tana kokarin hada kai da gwamnatin kasar Somaliya, domin tabbatar da tsaron jama'ar kasar, gami da taimakawa kokarin gina kasar, da shimfida zaman lafiya, a yanzu ke fusknatar barazana.
Don hake ne kwamitin ya yi tofin Allah-tsine ga harin da dakarun kungiyar Al-Shabab ta kaiwa sansanin rundunar ta AMISOM a wannan karo. Haka zalika, kwamitin sulhun ya isar da jajensa ga AMISOM, da gwamnatin kasar Somaliya, gami da jama'arta don gane da rasuwar mutane a sanadin harin.
Ban da haka, kwamitin ya nanata kudurinsa na ci gaba da aiwatar da manufofin MDD, na kokarin dakile duk wani irin aiki na ta'addanci, bisa la'akari da yadda ayyuka na ta'addanci suke mummunar barazana ga tsaro da zaman lafiyar duniya.
Kafin hakan rundunar AMISOM ta sanar da cewa, an kaiwa sansaninta farmaki, wanda ke dab da filin saukar jiragen sama na Mogadishu a ranar 25 ga wata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojojin kungiyar AU 3, da wani farar hula daya. Tuni dai kungiyar Al-Shabab ta sanar da daukar alhakin wannan farmaki. (Bello Wang)