A yayin wannan ziyara, mambobin tawagar dake kunshe da wakilin dindindin na kasar Ingila dake MDD, Mark Lyall-Grant da kuma jakadan Najeriya Usman Sarki, sun gana da shugaba Hassan Sheik Mohamud, firaminista Abdiweli Sheik Ahmed da kuma sauran manyan jami'an Somaliya. Haka kuma tawagar ta samu tattaunawa tare da wakilan tawagar MDD (ONUSOM) da kuma na tawagar tarayyar Afrika dake Somaliya (AMISOM) da kuma mambobin kungiyoyin fararen hula, in ji ONUSOM a cikin wata sanarwa.
Wannan ziyara ta zo a wani muhimmin lokaci ga kasar Somaliya, a yayin da kasar take shirin kaddamar da mataki na gaba game ayyukan soja domin yaki da kungiyar Al-Shabaab, haka kuma kasar na fuskantar matsalar jin kai da kuma sauye sauyen siyasa da zummar kafa wani salon mulkin tarayya, in ji tawagar MDD.
Mambobin kwamitin sun kuma bayyana fatansu na ganin gwamnatin tarayyar Somaliya ta kafa wani kwamitin zaben mai zaman kansa cikin gaggawa, da kuma maida hankali kan gyaran fuska ga kundin tsarin mulki da kuma shirya zaben raba gardama kan wannan batu nan da karshen shekarar 2015 da kuma shirya zabubuka a shekarar 2016. (Maman Ada)