in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta sake bude ofishin jakadancin ta a kasar Somaliya
2014-10-13 20:21:15 cri
Yau Litinin 13 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin Hong Lei ya bayyana cewa, a kokarin kara bunkasa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa kasar Sin ta sake bude ofishin jakadancin ta a kasar Somaliya a ranar lahadin nan 12 ga wata tare da nada sabon jakada.

A wannan rana a gun taron manema labaru, Hong Lei ya bayyana cewa, gwamnatin Sin ta nuna goyon baya ga yunkurin shimfida zaman lafiya da samun farfadowa bayan yaki. Don haka ta yi imani cewa, za a bude wani sabon babi wajen bunkasa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata. Haka kuma kasar Sin na fatan kara kokari tare da Somaliya wajen karfafa mu'amala da sada zumunci, domin kara kawo alheri ga jama'ar su.(fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China