Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya umurci rundunar sojojin kasar ta Amurka da ta kara tura dakaru 1,500 zuwa Iraki domin baiwa rundunar sojojin Iraki horo da taimako.
Wata sanarwa wacce ma'aikatar tsaron Amurka ta gabatar ta ce, Obama ya umurci ministan tsaron kasar Chuck Hagel da ya tura Karin dakarun Amurkar zuwa Iraki, amma a matsayin masu taimako ba'a matsayin mayaka ba, a cikin watanni masu zuwa.
Sanarwar ta ce, kara yawan sojojin Amurka a kasar Iraki zai taimaka wajen fadada kokarin da Amurkar take yi na baiwa sojojin Iraki cikakken horo.
Kakakin ma'aikatar tsaron Amurka John Kirby ya ce, ministan tsaron kasar Chuck Hagel ya baiwa shugaba Obama shawarar daukar matakin kara aikewa da dakaru zuwa Iraki, a sakamakon bukatar hakan daga gwamnatin Iraki, kimar da babbar hedkwatar rundunar sojan Amurka ta yi, da ci-gaban da sojojin Iraki suka samu a filin yaki, kuma hakan ya yi daidai da shirin hadin gwiwa na kare muhimman wurare da kuma kai hare-hare kan kungiyar ISIS. (Suwaiba)