in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Amurka ya bada umurnin kara tura dakaru zuwa kasar Iraki
2014-09-03 15:54:22 cri
A jiya Talata 2 ga wata ne, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bada umurnin kara tura dakaru kimanin 350 zuwa kasar Iraki, fadar shugaban kasar wato White House ta bayyana cewa, manufar tura wadannan dakaru ita ce kare ofisoshin jakadanci da ma'aikatan kasar Amurka dake birnin Bagadaza.

Kakakin fadar shugaban kasar Amurka Josh Ernest ya bayyana cewa, an dauki wannan mataki kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta bukata, wannan ya sa shugaba Obama ya umurci ma'aikatar tsaron kasar da ta kara tura dakaru zuwa kasar Iraki, wadanda ba za su shiga yaki a kasar ta Iraki ba. Kuma bayan da dakarun suka isa, wasu dakarun kasar Amurka da aka jibge a kasar Iraki a da za su janye daga kasar.

Hakazalika kuma, Mr Ernest ya bayyana cewa, shugaba Obama ya ce, zai dauki matakan da suka wajaba don kare dukkan ofisoshin jakadanci da ma'aikatan kasar dake sassan daban-daban na duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China