in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurkawa fiye da 100 suna wa kungiyar ISIL aiki
2014-09-04 15:31:35 cri
Ministan tsaron kasar Amurka Chuck Hagel ya bayyana wa 'yan jarida a ranar 3 ga wata cewa, yanzu akwai Amurkawa fiye da 100 da suke aiki ga kungiyar ISIL a yankin gabas ta tsakiya.

Hagel ya bayyana a wannan rana cewa, akwai mutane fiye da 100 da ke rike da passport din Amurka a cikin kungiyar ta ISIL, lamarin da ke kawo babbar barazana ga tsaron kasar Amurka, don haka, ya sake jaddada burin da sojojin kasarsa ke neman cimmawa a matakan da suke dauka a Iraki.

Shugabar kwamitin sulhu na MDD na wannan karo kuma zaunanniyar wakiliyar kasar Amurka a MDD Samantha Power ta bayyana a ranar 3 ga wata cewa, shugaban kasar Amurka Barack Obama zai shugabanci taron kwamitin sulhun a ranar 25 ga wata, inda zai nemi goyon bayan kwamitin sulhun ta yadda za a hana 'yan ta'adda kasashen waje shiga rikicin da ke faruwa a sauran kasashen duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China